Nan Da Wata 14 Sojojin Amurka Zasu Bar Afghanistan

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani, ya fitar da wata doka da za ta bayar da damar fara shirin sakin dubban fursunoni mayakan Taliban yayin da rundunar sojin Amurka ke fara janye dakarunta daga kasar, wannan wani bangare ne na yarjejeniyar da aka kulla da kungiyar Taliban da niyyar kawo karshen yakin da aka shafe kusan shekara 19 ana yi.

Yarjejeniyar tsakanin Amurka da Taliban, wacce aka sanya wa hannu a Qatar kwanaki 10 da suka gabata, ta bukaci dukan sojojin Amurka da na kawancen kasashe da su fice daga kasar a cikin watanni 14 masu zuwa, bisa sharadin cewa kungiyar Taliban za ta dauki matakan yaki da ta’addanci ta hanyar bin hanyoyin siyasa wajen warware takaddamarta da sauran masu ruwa da tsaki a Afghanistan.

Wani mai magana da yawun sojojin Amurka, Kanar Sonny Leggett, ya ce rundunar sojin Amurka a Afghanistan ta fara rage yawan sojojinta daga kusan 13,000 zuwa 8,600.