"Deash tana tsamurewa.Kuma za'a yi galaba akanta," inji Holland, ya kira kungiyar da lakabin da ake kiranta da labaraci.
Sa'o'i bayanda Holland isa Iraqi a jiya Litinin, bam ya tashi a wata kasuwa dake unguwar Sadr dake gabashin birnin dake shake da leburori. Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.
A lokacin da suka yi taro da menama labarai tareda shugaban na Faransa, PM Iraqi Haider al-Abadi, yace maharin ya shigo kasuwar a zaman wand a yake son ya dauki lebori aiki, daga nan ne ya tada bam din.
Haka nan Holland ya gana da shugaban kasar na Iraqi na jeka na-yi ka Fuad Masum, daga bisani ya ziyarci yankin arewacin kasar na kurdawa mai kwariya-kwariyar cin gashin kai har ya gana d a shugabannin yankin.
Shugaban na Faransa ya kuma ziyarci sojopjin kasarsa a Bagadaza, da kuma wadanda suke yankin Kurdistan wadanda suke taimakawa a fafatawar da da ake yi d a 'yan kungiyar ISIS., ya gayawa dakarun cewa kokarinsu yana taimakawa wajen hana akai musu hare-haren ta'addanci a can kjasarsu.