Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirinta na kara kudin kiran waya da data sai dai ta baiwa al'ummar kasar tabbacin cewa ba zai kasance 100 bisa 100 ba kamar yadda kamfanonin suka nema.
washington dc —
Ministan Sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani, Bosun Tijjani, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a Abuja a jiya Laraba.
Ya kara da cewa hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta bullo da tsare-tsare game da sauye-sauyen haraji a bangaren kamfanoni sadarwa.
A cewarsa, mun yi la'akari da abubuwa da dama akan yadda zamu tabbatar mun bada gudunmowa mai ma'ana domin ci gaban Najeriya.
"A makonnin da suka gabata, an samu kiraye-kiraye daga wadannan kamfanonin sadarwa na yin karin haraji, inda suka bukaci ayi karin zuwa kaso 100. Wannan ba al'amari ne da za mu amince da shi ba a halin yanzu a matsayinmu na gwamnati.