Naman Zomo Zai Iya Samun Karbuwa a Afirka Nan Gaba

A hankali dai, naman zomo na kokarin ya zama naman da ake ci a ko ina a Afirka, yayin da ya samu inganta a masana’antu a Afirka ta Kudu da Najeriya, kuma gungun manoma na Zomaye suna inganta naman da cewa ya na da arha da kyau ga lafiyar jiki da kuma muhalli. Amma kuma, zai kuwa samu karbuwa? Masu suka sun ce sun ƙi cin dabbobin da ake ganin dabbobin zaman cikin gida ne.

Manoma na Afirka na neman mafita game da sha’awar cin nama a nahiyar. An kimanta yawan mutanen Afirka kusan ninki biyu a cikin shekaru uku masu zuwa, zuwa biliyan 2.5.

A cikin shekaru goma da suka gabata, babban kamfanin samar da naman Zomo na Afirka ta Kudu ya kara kusan gonaki na Zomaye 150 a cikin gonar san a dabbobi.

Manomi mai zaman kansa Gavin Grgurin yana ajiye da zomaye 500 a gonarsa a wajen Johannesburg. Ya ce yana tsammanin naman zai samu karbuwa nan gaba ne.

Na daya, in ji shi, naman Zomo yana samar da sinadarin gina jiki da kuma rashin kitse. Ba sa bukatar babban wurim kuma ba sa cin abinci da yawa. Ba sa buƙatar ƙasa da ruwa sosai kamar da kaji, kuma kashinsu kadan ne ba kaman shanu ba. Zomaye, in ji Grgurin, na iya zama mara ila a duniya.

Amma shin zasu iya yin tsalle daga dabbar zaman gida zuwa na ci a gida?

Manajan Kasuwancin Sloane Meat Richard Letcher ya ce ya lura da sha'awar nama na 'yan Afirka ta Kudu yana karuwa. Shagon sa na ɗaya daga cikin shagunan a Johannesburg da ke sayar da Zomo, amma kasuwanci na tafiya a hankali.

"Abin da ya canza a cikin yanayin mu a bara shine yawan buƙatun naman akuya da ya karu."

Ya bada dalilin naman zomo, wanda a yanzu kasuwanci na dan tafiya a hankali, zai iya fadada.

Amma to shin shi ya tabi cin naman? Ya fadi dalili guda da mutane ke bayarwa na rashin cin zomo.

"A yanzu ban sa tunanina ta yadda zan iya cin daban da ke zaman cikin gida ba, don haka, a'a."

Abokin aikinsa, mai yanka nama Mnelisi Smakade, ya ce bai san dadi ba. Shi yana son naman zomo. Babban tambaya a nan itace:

"Yana da dandano kamar kaza. Misalin kaji. Ba shi da tauri kamar naman saniya. Ya na dadi da kuma laushi."

Yayin da yawan jama'ar Afirka ke dab da kusan ninki biyu zuwa shekara ta 2050, wadatar abinci - musamman furotin - babbar damuwa ce. Shin zomo zai iya wadatar da cikin miliyoyin jama’a?

Wakiliyar Muryar Amurka, Anita Powell ta hado mana rahoton daga Johannesburg.