A rayuwa kusan kowa na fuskantar kalubale a fannoni daban-daan, amma duk wani kalubale da dake tattare da nakasa, baban kalubale ne.
Malama Khadija Abubakar, dake zaune a jihar Kano na daya daga cikin matan dake fuskantar baban kalubale a rayuwa kasancewarta gurguwa sanadiyar cutar shan Inna. A wata hira da wakiliyar muryar Amurka Baraka Bashir, Khadija ta bayyana mata yadda take gudanar da harkokin yau da kulum.
“Wani hannin ga Allah Baiwa ne, cikin hikimar sa (Allah) in ya hana ka wani abun sai ya baka wani” inji malama Khadija. Ta kuma ce dole ne abubuwa dayawa su gagareta tun da bata da kafa amma tana da ‘yaya dake taimaka mata matuka.
Abin tausayi shine daya daga cikin ‘yayan Khadija shima yana fuskantar matsalar ta shan inna, abinda uwarta ce ya tada mata hankali sosai musamman in ta tuna irin wahalhalun da ta fuskanta kafin ta sami iyali. Duk da kalubalen da malama Khadija ke fuskanta, ta kan gungura dan kekenta ta kai Dan asibiti don nema masa magani da gashi har na tsawon shekara guda, bayan da ta sami juna biyu.
Amma duk da halin rayuwar da malama Khadija ke ciki, babu abinda ya gagareta, don kuwa har sana’ar saida abinci tana yi.
Your browser doesn’t support HTML5