Bara a nahiyar Afirka na ci gaba da samun dakushewa ga al’umma musamman yadda ake ta kokarin taimakawa nakasassu don inganta musu rayuwar dogaro da kai.
WASHINGTON D.C —
Kungiyar kasa da kasa da ke taimakawa nakasassu a jamhuriyar Nijar sun bada tallafin kayayyakin sana’o’in hannu ga nakasassu a kasar.
An gudanar da bada taimakon ne karkashin jagorancin Magajin Garin Yamai Hamma Saidu, inda ya yi kira ga cewa a taru a ci gaba da taimakawa Nakasassu don fidda su ga halin kunci.
Nakasassun suma sun ji dadin al’amarin na taimakawar, musamman da magajin garin yace, za su mika bukatar tunawa da nakasassun a maganar kasafin kudin kasar don tallafa musu.
Your browser doesn’t support HTML5