Nakasassu A Borno Sun Sami Tallafi A Ranar Tunawa Da Su Ta Duniya

Masu fama da nakasa a Nigeria

Ranar uku ga watan Disamban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da wadanda suke da nakasa, kama daga guragu da makafi da kurame da kutare. Wadannan masu lalura suna dogara ne da barace barace domin wajen gudanar da harkokin rayuwar su.

Ana tuna wannan rana ta masu fama da nakasa ne tun cikin shekarar 1992, lokacin da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar uku ga watan Disamba a matsayin ranar nakasassu. Ana amfani da wannan rana ne wurin kyautata rayuwa da kula da hakkokin masu fama da nakasar ko a ina suka kasance, yayinda ake jaddada wayar da kan jama’a a kan hali da masu fama da nakasa ke ciki tsakanin al'umma, da fagen ci gaba da zamantakewa da fannin tattalin arziki da kuma al’adu.

Bukin ranar masu fama da nakasa ta duniya na bana ya mayar da hankali ne a kan tallafawa rayuwar masu fama da nakasar ta yadda za a yi aiki tare da su da basu ilimi da kuma samar musu cigaba mai dorewa kamar yadda shirin Majalisar Dinkin Duniya na cimma muradu cigaba mai dorewa kafin shekarar 2030 ya tanadar, wanda ya kuduri aniyar tafiya da kowa kana ya yiwa nakasassu tanadi.

Hukumomi a kasashen Afrika masu tasowa su kan bada tallafi ga masu fama da nakasar domin rage musu da wahalhalu da su kan tsinci kansu a ciki. Gwamnatin jihar Borno a Najeriya tana daukar matakan kyautata rayuwar masu nakasa a jihar ta hanyar basu tallafin Naira dubu talatin cikin watanni shida.

Ga dai rahoton Haruda Dauda daga Maiduguri:

Your browser doesn’t support HTML5

RANAR MASU FAMA DA NAKASA