Najeriya Zata Kafa Kamarorin Binciken Tsaro a Birane,

Ganawar Shugaba Trump da 'yammatan Chibok

Saboda tabarbarewar tsaro a Najeriya da duniya ma gaba daya shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana shirin saka kamarorin binciken tsaro a birane domin zamanatar da harkokin tsaron

Idan ba'a manta ba yayinda yake jawabi a taron tsaro da rundunar 'yansandan kasar ta shirya ya bayyana kara 'yansanda dubu goma saboda inganta tsaron.

Shugaba Buhari yace za'a kafa naurorin domin zama cikin shirin ko ta kwana idan an gano wata gadar zare.

Mukarabin shugaban Sanata Hadi Sirika yayi karin haske kan sabon shirin. Yace bai yiwuwa a yi yaki da miyagun ayyuka ba tare da kimiya da fasaha ba.

Gwamnatin da ta shude tayi kokarin kafa naurorin amma ta kasa domin akwai wadanda suka fi karfin doka a lokacin. Shugabannin da ne suka bari lamarin ya tabarbare.

Dangane da ko shirin zai yi tasiri idan aka yi la'akari da dimbin kudin da ake bukata da kuma kudin karin 'yansanda dubu goma Hassan Gimba editan jaridar Leadership ta ranar Juma'a yayi furuci a kai. Yace kawo yanzu babu abun da shugaba Buhari yace zai yi da bai yi ba.

Idan yace zai kafa naurori a biranen kasa ya san inda zai samo kudaden ya yi su. Kada a manta ya fita kasashen waje kuma sun yi mashi alkawari a kan inganta tsaro a kasar. An yi mashi alkawari duka abun da ya shafi tsaro zasu taimaka.

Ita naurar da za'a kafa zata maye gurbin wani mahimmin abun da ake dashi da yanzu kuma babu shi. Da ana da masu tsaron cikin gida kowane mutum ya sa ido kan wadanda ke shigowa. Yanzu babu irin hakan. Naurorin su ne zasu sa ido kan abubuwan dake faruwa..

Misali a Bankok an tada bom amma naura da aka kafa ta gano wanda ya haddasa ta'asar. Ga hotonsa a koin ana nemansa. Naurar zata taimaka. Masu dubata zasu gani idan wani ya ajiye wani abu su kira 'yansanda su gaya masu.

Ga karin bayani daga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Zata Kafa Kamarorin Binciken Tsaro a Birane