Ministan ilmin Najeriya, Malam Adamu Adamu yace Gwamnatin kasar zata dauki matakan dadawa malamai da kuma inganta shi kansa aikin malanta don karfafa sha’anin ilmi.
Sai dai kuma Ministan ya bukaci gwamnonin jihohi tare da masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi su hada karfi da karfe domin habaka ilimi a kasar.
Yanzu haka wasu jihohi sun soma daukan matakan inganta ilimin da kyautatawa malamai rayuwa kamar yadda yake faruwa a jihar Gombe, wadda gwamnanta Ibrahim Hassan Dankwambo yace ya kafa kwamitin musamman kan gyara makarantu.
Ita ma Kwamishanar ilimin jihar Gomben, Hajiya Amina Muhammad Ahmed, ta ce an fito da shirin baiwa iyaye mata tallafi domin yara mata su daina talla, su samu su je makaranta.
Daliban da aka zanta dasu sun tabattarda cewa lalle an samu chanje-chanje a fannoni da dama da suka hada da fannin kayan karatu da abincin da ake basu.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5