Najeriyar na shirye-shiryen sake bude filayen jiragenta domin sufurin kasa-da-kasa a ranar 29 ga watan Agusta, tun bayan da ta rufe a watan Maris, kuma tana kara karfafa dokoki na sake bude zirga-zirgar.
Minista Hadi Sirika ya fadawa wakilan kamfunan sufurin jiragen sama cewa Najeriya za ta maida martanin haramta shigowar ‘yan wasu kasashe da suka hana ‘yan Najeriya shiga kasashensu, dokar da kuma za ta yi aiki ga dukkan kamfanonin jiragen da kuma dukkan ‘yan kasashe.
Sirika ya ce “idan kuma kasashen sun hana ‘yan Najeriya da ma jiragen saman Najeriya shiga, to mu ma haka za mu yi wa nasu.”
Wani mai magana da yawun Ministan ya fada kwana daya baya cewa, dokar ta rama-takwarkwara za ta shafi ba da damar saukar jirage a maimakon ‘yan kasar. To sai dai Sirika ya ce za’a dauki matakin ne domin yin adalci ga ‘yan Najeriya.
Sirika ya kara da cewa “adadin masu cutar COVID-19 ko kusa bai kai yawan na wasu kasashe da muka gani ba a Turai,” inda ya ce wannan dokar ta haramtawa 'yan kasarmu shiga wasu kasashe tamkar “nuna bambanci ne ga mutanenmu.”
Najeriya tana da wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 50,951, da kuma adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar 992.