Najeriya Za Ta Kashe Fiye da Naira Tiriliyon Biyar Wajen Sake Gina Arewa Maso Gabas

Onarebul Yusuf Captain Baba shugaban kwamitin sake gina arewa maso gabas na shugaban kasa yayinda yake zantawa da Muryar Amurka

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kashe sama da naira tiriliyon biyar wajen sake gina arewa maso gabas da ‘yan ta’adda ta Boko Haram ta lalata.

Shugaban karamin kwamitin shirin shugaban Najeriya na sake gina yankin arewa maso gabas Hon. Yusuf Captain Buba mai wakiltar mazabar Hong da Gombi ya ba da bayanin haka a wata hira da ya yi da Muryar Amurka a Yola fadar jihar Adamawa lokacin da ya ke amsa tambayar dalilan da suka sa shirin ke tafiyar hawainiya wanda ya danganta da rashin sanya hanu kan kasafin kudin bana.

Shirin sake gina arewa maso gabas inji Hon. Yusuf Captain Buba zai hada da gina asibitoci, makarantu, wuraren ibada, samar da muhimman kayan jin dadin rayuwa,tsaro, wutar lantarki, samarwa mata da matasa jari da kuma tallafi ga ‘yan kasuwa da suka yi asarar hajojin su.

Matsalar rashin wutar lantarki a yankunan da Boko Haram ya shafa inda suka tarwasa tiransfomomi da lalata wayoyin wuta, gwamnatin tarayya za ta kashe sama da naira biliyan tara inji injiniya Umar Baba Mustapha babban manajan kanfanin samar da wutar lantarki a arewa maso gabas dake da ofishinsa a Yola fadar jihar Adamawa.

Ya ce a birnin Maiduguri kadai Boko Haram sun farfasa tiransfomomi sama da saba’in kana kuma suka lalata na’urar da ke baiwa birnin Difa a jumhuryar Nijar wutar lantarki. Daya daga kafar dake samarwa Najerya kudaden musaya da kasashen waje.

Garuruwan da matsalar rashin wutar lantarki ya shafa sakamakon barnar da Boko Haram suka haddasa sun hada da Dambuwa, Bama, Askira Uba, Madagali , Gulak, Gwoza da Michika.

Ga Sanusi Adamu da kari bayani a rahotonsa.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Za Ta Kashe Fiye da Naira Tiriliyon Biyar Wajen Sake Gina Arewa Maso Gabas - 2' 58"