Najeriya Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kasashen Yankin Tafkin Chadi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Idris Deby na Chadi (Garba Shehu)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na shirin karbar bakuncin taron shugabannin kasashen da ke yankin tafkin Chadi, taron da zai mayar da hankali kan shawo kan matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram.

Za a gudanar da taron kolin ne a ranar 12 ga watan nan na Yuni, a gefen bikin rantsar da shi a wani sabon wa’adi na biyu bayan da ya lashe zabe.

Yayin da suke wata ganawa da shugaba Idris Deby Itno na kasar Chadi a Saudi Arabia, inda shugabannin biyu suka halarci taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC, Buhari ya bayyana cewa, lokaci ya yi da za a shata sabbin hanyoyi tunkarar kungiyar a yankin.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ta nuna cewa, yanzu Buhari zai samu karin lokacin tunkarar barazanar kungiyar tun da an kammala zabe.

A tattauwanar da shugabannin biyu suka yi, sun tabo batun yadda yanayi na ruwan sama yake kawo cikas ga ayyukan soji wajen yakar ta’addanci a yankin, lamarin da ya sa suka ce akwai bukatar a bullo da wasu sabbin dabarun tunkarar mayakan.