Taron da za a gudanar karo na farko a nahiyar Afirka, a zai yi nazari akan hanyoyin bunkasa safarar kayan da ake shigowa da su kasashen yankunan da babu tashoshin ruwa ta hanyar amfani da mota da kuma jiragen kasa.
Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Najeriya Hajiya Hadiza Bala Usman, wacce ita ce mataimakiyar wannan kungiyar, ta ce taron shine na farko da aka shirya za’a gudanar a Nahiyar Afrika.
Haka-zalika kakakin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan ya bayana cewa mukasudin wannnan taron shine don a duba yadda za’a rika safarar kayan da ake shigowa da su daga Turai zuwa cikin kasa ko wasu kasashen da basu da tashoshin jiragen ruwa domin samun riba.
Shugabar Hukumar Tashohin Jiragen Ruwa Hajiya Hadiza Bala Usman, ta yi Karin bayani, cewa “kokarin da hukumar take yi na safarar kayan da ake shigowa da su dake kasashen waje zuwa yankunan arewacin Najeriya, ya zama dole a yi amfani da jirgin kasa, wajen kwasar kayan daga tashoshin jiragen ruwa zuwa cikin kasa, ta haka ne kawai za’a samu ragewar cinkoso kuma a samu biyan bukatar gudanar da kasuwanci”.
Your browser doesn’t support HTML5