Najeriya tayi barazabar kai karar Iran gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Wani sojan Najeriya a hannun dama yana nunawa yan jarida makamai a Lagos ranar Laraba, 27ga watan Oktoba, 2010. Irin wadannan makaman rokan ne mayaka ke amfani da shi a a Afghanistan suna daga cikin makaman da aka yi fasakwaurinsu zuwa Najeriya a cikin k

Jami’an Najeriya sun ce zasu kai karar kasar Iran gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya idan suka sami tabbacin cewa an keta dokar kasa da kasa da kuma takumkumin Majalisar Dinkin Duniya wajen shigar da makamai kasar.

Jami’an Najeriya sun ce zasu kai karar kasar Iran gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya idan suka sami tabbacin cewa an keta dokar kasa da kasa da kuma takumkumin Majalisar Dinkin Duniya ta wajen fasakwaurin makamai zuwa Najeriya da ake zargin cewa sun sami asali daga kasar Iran. Ministan harkokin kasashen ketare na Najeriya Odein Ajumogobia ne ya bayyana haka yau. Ministan ya gana da takwaranshi na kasar Iran Manouchehr Mottaki jiya da maraice a birnin tarayya Abuja domin tattaunawa kan batun makaman da aka shigar Najeriya. Ajumogobia yace Mottaki ya ba jami’an Najeriya izinin yiwa daya daga cikin Iraniyawa biyu da ake zargi da hannu a shigo da makaman tambayoyi. Jami’an leken asirin Najeriya sun kama kwantenoni dankare da makamai a Lagos makonni biyu da suka shige, suka kuma tarar makaman sun hada da roka-roka da manyan bindigogin igwa da gurneti da kuma nakiyoyi iri dabam dabam.