Najeriya Tana Shirin Kafa Dokar Haramta Nunawa Masu Kanjamau Wariya

Ana lura da wasu masu kanjamau

Gwamnatin Najeriya ta fara daukar matakin kafa dokar da zata haramta nunawa wadanda suke dauke da cutar HIV wariya.

Cibiyar yaki da cutar kanjamau ta kasa da ake kira a takaice NACA ce ta bayyana haka yayin wani zama da masu ruwa da tsaki a Abuja.

Darektan cibiyar Farfesa John Idoko wanda ya jagoranci zaman ya bayyana cewa, ya zama tilas Najeriya ta gabatar da tsarin da kungiyar ECOWAS ta cimma da kungiyar ta gabatar ga majalisar wakilai.

Dokar zata haramta nunawa masu fama da cutar kanjamau wariya ko take hakkokinsu.
Frofesa Idoko yace wariyar da ake nunawa masu dauke da cutar yana da alaka da yaduwar cutar, ya kuma ce ana tauye hakin masu fama da cutar sau da dama abinda yake kara sa cutar da wahalar da su.