A lokacin wata hira da muryar Amurka , Alhaji Abubakar Chika tsohon jakadan Najeriya a kasar Iran cewa yayi Najeriya tayi rawar gani wajen daukar matakin da ta dauka saboda hakan zai sa sauran kasasahen da abin ya sha daukar mataki don nuna wa gwamnatin Afrika ta kudu ta gyara dangantakarta da sauran kasashe musamman ma na Afrika.
Duk da cewa Afrika ta kudu tayi Allah wadarai da kissan gillar da akayi wa bakin, Alhaji Abubakar ya fadi cewa har yanzu babu wani abin da kasar tayi game da basaraken da yayi jawabin daya haddasa tashin hankalin. Duk da cewa dai basaken na Zulu, yace an yi wa jawabin nasa bahaguwar fahimta ne.
Shekaru kusan talatin da suka wuce, lokacin mulkin Janar Mohammadu Buhari na farko, Najeriya da kasar Isra’ila basu da wata danganta. Sarkin Kano a lokacin da sarkin Ife suka je kasar amma daga baya sun fuskanci hukuncin gwamnati. Abinda ya kamata duk wani shugaba adili yayi kenan, a cewar tsohon jakadan.
Alhaji Abubakar ya kara da cewa duk da dai Najeriya bata ji dadin abin da ya faru ba, ‘yan Najeriyar ma ba kanwar lasa bane don duk wata ta’asa, ko aikin assha da aka yi a Afrika ta kudu zaka ga dan dan Najeriya a ciki musamman ma a gidajen kasonsu, inda abin takaici akwai ‘yan Najer iya sosai.
Your browser doesn’t support HTML5