Najeriya Ta Shiga Yarjejeniyar Cinikayya Tsakanin Kasashen Afirka

Lokacin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ke sanya hannu a yarjejeniyar AfCFTA

Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta ba kasashen Afirka damar yin kasuwanci a tsakaninsu ba tare da wata tangarda ba.

A yau Lahadi, Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sanya hannu a wannan yarjejeniya a birnin Yamai da ke Jamhuriyar Nijar yayin taron kungiyar kasashen tarayyar Afirka na AU, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun Shugaba Buhari Femi Adesina, wacce Muryar Amurka ta samu ta hanyar email.

“Yanzu na samu karramawar sanya hannu a yarjejeniyar da za ta samar da walwala a fannin kasuwancin nahiyar Afirka ta (AfCFTA), a madadin kasata Najeriya.”

Sai dai sanarwar ta kara da cewa, Buhari ya jaddada muhimmancin ganin an aiwatar da wannan yarjejeniya cikin kyakkyawan yanayi.

“Najeriya na so ta nanata cewa dole ne walwalar yin kasuwanci ta zamanto an yi ta cikin kyakkyawan yanayi, a matsayinmu na shugabannin Afirka, ya kamata hankulanmu su karkata wajen aiwatar da yarjejeniyar ta hanyar da tattalin arzikinmu zai bunkasa da samar da ayyukan yi ga matasanmu.”

Ita ma Jamhuriyar Benin ta amince ta rattaba hannu akan wannan yarjejeniya bayan da ta ki amincewa a baya.

Rattaba hannun da Najeriya da Benin suka yi, na nufin yanzu kasashen nahiyar 54 cikin 55 sun amince da yarjejeniyar, illa kasar Eritrea wacce ta zama kasa tilo da ba ta cikin wannan yarjejeniya.

A baya, Najeriya ta janye daga yarjejeniyar, inda ta yi korafin cewa kasancewa a cikinta zai kassara fannin kananan masana’antunta, sannan za a mayar da Najeriya tamkar shara, inda za a rika shiga da kowanne irin kaya.