Najeriya Ta Shiga Jerin Sunayen Kasashe Marasa Tabbas

Shugaban Najeriya da mataimakinsa

Fitowar Najeriya a jerin kasashe marasa tabbas a duniya da asusun zaman lafiya dake birnin Washington DC ya bayyana a rahotansa na nuna yadda sunan Najeriyar ke daukar hankalin cibiyoyin bincike dana tattalin arziki da lamurrran labaru musammman ma ta fuskar tsaro.

Asusun dai yace don faduwar darajar fetur da kuma illar ‘yan Boko Haram, Najeriya ta jera sahu daya da sauran kasashe irin su Afghanistan da Pakistan da ma na cikin Afirka irinsu Zimbabwe da Guinea, a cewar asusun lamuran Najeriya sun ta’azzara a shekarar da ta gabata.

Hakanan kuma saboda lamuran yanayin yaki saboda ta’addancin ‘yan Boko Haram, rayuwar ‘yan Najeriya ta shiga sahun irin mutanen Somalia da Jamhuriyar Dimokaradiyar Kongo da Yaman da Sudan ta Kudu.

Imran Adam, lauya ne a birnin Abuja wanda ke ganin kamar akwai yanayi na rashin adalci cikin wannan rahotan, kasancewar Sudan ta Kudu ta dade rabonta da kwanciyar hankali a kasar bai kamata ba ace an hada ta da Najeriya ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Shiga Jerin Sunayen Kasashe Marasa Tabbas - 3'00"