A wani al'amari na tarihi, Najeriya ta samu zababbiyar gwamnar jaha mace ta farko, wadda ba ma daga kudancin kasar ta fito ba; daga arewacin kasar ta fito - inda ada ake ganin hakan da matukar wuya.
Wannan al'amarin, wanda rahotanni ke nuna cewa ya faranta wa jama'a da dama - musamman ma mata da matasa da sauran ma'abuta canji - rai, ya biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka kara ta Tarayya da ke babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja ta yanke dazu-dazun nan, inda ta ayyana Sanata A'isha Jummai Alhassan a matsayin Gwamnar jahar Taraba.
Ga wakilanmu Hassan Maina Kaina da Ibrahim Abdul'aziz daga Abuja da Taraba da cikakkun rahotannin:
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5