Najeriya Ta Sami Karin Mutum 481 Da Suka Kamu Da COVID-19

Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya, (NCDC), ta fitar da alkalumma a kan yakin da take yi da yaduwar COVID-19 a wani sakon Twitter a jiya Alhamis.

Sabbin alkaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa an samu karin daruruwan mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.

A cewar hukumar, mutum 481 ne cutar ta harba a ranar Alhamis 30 ga watan Yuli, wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 42,689.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 19,207 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 878 suka mutu.

An samu sabbin alkaluman ne daga jihohi 15 kuma birnin Tarayya Abuja ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus, da mutum 96. Sai jihar Lagos da ke bin ta da mutum 89.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da jihar Plateau da Karin mutum 68, Ogun - 49, Edo - 44, Rivers - 43, Oyo - 25, Osun - 23, Delta - 15, Enugu – 11, Kano – 7, Kaduna – 7, Bauchi – 2, Bayelsa – 2, Yobe - 1.