Dan wasan Golden Eaglet Victor Osimhen ne ya fara zirawa Najeriya kwallonta kana jim kadan Funsho Bamgboye ya kara wata kwallon.
Gabanin zira kwallayen, Najeria ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda Osinachi Ebere ya buga ya zubar.
Dan wasan Najeriya Osimhen shi ne dan wasan da ya lashe kyautar wanda ya fi zira kwallaye a gasar da kwallaye goma, wanda ba a taba samun dan wasan da ya yi haka a baya ba.
Wannan shin ne karo na biyar kuma da ‘yan wasan Golden Eaglet ke lashe wannan kofi kuma Najeriya ce kasa ta biyu da ta taba lashe kofin sau biyu a jere.
Baya ga haka wannan shi ne karo na takwas da Najeriya ke kaiwa ga wasan karshe a wannan gasa.
A shekarar 1985 Najeriya ta fara lashe kofin gasar a lokacinmulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya na mulkin soja.
Waklin Muryar Amurka, Murtala Faruk Sanyinna ya mana dubi kan tarihin yadda Najeriya ta lashe gasar sau biyar:
Your browser doesn’t support HTML5