Najeriya Ta Lallasa Kamaru Da Ci 3-2

'Yan wasan Najeriya suna murnar cin kwallo. APTOPIX

Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles. ta samu nasarar shiga zagayen gab da na kusa da na karshe, wato quarter finals bayan da ta doke Kamaru.

‘Yan wasan Najeriya sun doke takwarorinsu na Indomitable Lions ne da ci 3-2 a zagayen ‘yan 16 da aka shiga.

Hakan na nufin an yi waje-rod kenan da Kamaru a gasar, wacce ita ke rike kofin.

Najeriya ce ta fara zura kwallo a ragar Kamaru ta hannu dan wasanta Odion Ighalo.

Amma ‘yan wasan Kamaru sun yunkuro suka farke kwallon farko har ma suka kara wata ta biyu, lamarin da ya ba su damar shiga gaban Najeriya da ci 2-1 kafin a je hutun rabin lokaci.

Jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokacin ne Najeriya ta yi kukan kura ‘yan wasanta Ighalo da Alex Iwobi suka zura kwallaye daya-daya – lamarin da ya kai wasan ga 3-2, aka kuma tashi a haka.

Nan ba da jimawa, Masar mai masaukin baki za ta fafata da Afirka ta Kudu - wanda ya yi nasara shi zai hadu da Najeriya.