Najeriya ta kiyasta kashe Naira biliyan 4.7 a wani sabon shirin yaki da cutar Polio

Ana ba yara maganin cutar shan inna

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake ware naira biliyan 4.7 domin aiwatar da wani sabon shirin allurar rigakafin shan inna.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake ware naira biliyan 4.7 domin aiwatar da wani sabon shirin allurar rigakafin shan inna.

Ministan lafiya na kasar Farfesa Onyebuchi Chukwu ne ya bayyana haka a wajen wani dandalin ministoci da aka gudanar a birnin tarayya Abuja. Bisa ga cewarshi, za a aiwatar da shirin ne a matakin jihohi da kuma babban birnin tarayya.

Bisa ga cewarshi, za a gudanar da sabon shirin ne bayan kaddamar da kwamitin yaki da cutar shan inna karkashin jagorancin karamin ministan lafiya, wanda bisa ga cewarshi, ya banbanta da wadanda aka aiwatar a lokutan baya. Wannan shirin inji shi, zai bada dammar sa ido sau da kafa a aikin rigakafin.

Ministan ya kuma bayyana cewa, an kiyasta kashe Naira miliyan 47 wajen sayen gidajen sauro da aka jika da magani da ake kira LLINs, kuma tuni aka fara sayen gidajen sauron da nufin shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.

Ya kuma bayyana cewa, a shirye gwamnatin tarayya take ta bincike tsarin raba alluran rigakafi daga matakin tarayya zuwa mazabu. Ministan yana mai cewa, “tilas ne dukan wanda yake da hakin aiwatar da shirin rigakafin ya bayyana mana abinda yake yi da abinda aka bashi.”

Ministan ya jadada cewa, hare haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa ya haifar da kalubalar gaske a fannin kiwon lafiya a Najeriya, duk da haka yace, gwamnati ta lashi takobin shawo kan cutar kafin karshen shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.