Najeriya Ta Karfafa Mataken Kariya Daga Cututtukan Lassa Da Coronavirus

  • Saleh Shehu Ashaka

Fargabar yaduwar cutar LASSA da “CORONAVIRUS” ya sanya hukumomin Najeriya daukar karin matakan rigakafi.

Hukumomin lafiya a Najeriya sun girke jami'an lafiya a tashoshin jiragen saman kasar domin tantace masu shigowa daga kasashen waje don gudun shigowa da cutar CORONAVIRUS.

Hukumomin lafiya a Najeriya, sun karfafa mataken tsaro da kariya daga muggan cututtukan nan biyu na zazzabin Lassa, wacce ake dauka daga beraye da kuma cutar nan wacce take yaduwa kamar wutar daji kuma ta samo asali daga kasar China, wato CORONAVIRUS.

Daga cikin mataken da aka dauka game da cutar LASSA, jami’an lafiya na kara fadakar da al’umma akan tsabtace muhalli da toshe duk wata kafa da beraye za su shigo gidaje su yada kwayoyin cutar ga jama’a.

Ministan muhalli na Najeriya Mahmud Muhammad, ya karfafa aikin duba-gari ta hanyar ba da shawarin kare dukkan kayayyakin amfani da abinci ta inda beraye baza su taba ba.

Ga cutar CORONA VIRUS wacce tuni, ta lakume rayukan mutane da dama a China, Najeriya na bin matakan sanya ido kan duk bakin da za su shigo kasar musamman ta hanyar filayen jiragen sama.

Duk da cewa kawo yanzu, ba a samu wani dauke da cutar CORONAVIRUS a Najeriya ba, zazzabin Lassa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a wasu jihohin Najeriya ciki kuwa har da jami’an kiwon lafiya.

Don Karin bayani, a saurari cikakken rahoton Saleh Shehu Ashaka:

Your browser doesn’t support HTML5

Mataken Kariya daga Cututtukan Lassa da Coronavirus