Najeriya Ta Kammala Dawo da Alhazanta Baicin Marasa Lafiya

Alhazai

Najeriya ta gama jigilar duk alhazanta baicin wadanda basu da lafiya da aka barsu a karkashin kulawar ofishin jakadancin Najeriya dake Saudiya

Najeriya ta kammala jigilar alhazanta zuwa gida, in baicin wasu shidda da basu da lafiya da Hukumar Alhazai ta dankawa ofishin jakadancin kasar domin cigaba da kula da su.

A zantawar da yayi da manema labarai, shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Barrister Abdullahi Muktar Muhammad, yace ya yafewa duk wadanda suka dauka shi ne ya haddasa tsadar kujerar zuwa hajji, ba tsadar Dala ba.

Karamin jakadan Najeriya a Saudiya, Alhaji Muhammad Sani Inusa, ya godewa Allah da kammala aikin hajin ba tare da an fuskanci matsalar bata sunan Nigeria da masu shigar burtu da sunan alhazai suna safarar miyagun kwayoyi ba, suke janyowa ba.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Kammala Dawo da Alhazanta Baicin Marasa Lafiya - 2' 21"