Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyar magance matsalar tsaron dake addabar sassan Najeriya ta hanyar karfafa rundunonin yaki da masu tada kayar baya.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da jirgi mai saukar ungulu samfurin “ti29 atak combat helicopter da kuma wani samfurin “beecraft king air 360er”, a sansanin sojin sama a Makurdi, babban birnin jihar Binuwe tare da wani jirgin dakon kaya da zai taimaka wajen karfafa ayyukan rundunar ta sama a kokarinta na fatattakar ‘yan ta’adda.
Mataimakin Shugaban Kasar ya samu jinjina daga jama’a a yayin da yake kaddamar da jirgin yaki samfurin “T129 atak helicopter”, inda aka gudanar da atisayen gwajin yadda yake aiki da kuma saukin sarrafarwarsa a cikin iska.
Gwamnan Jihar Binuwe, Hyacinth Alia, ya yabbawa gwamnatin tarayya tare da bayyana fatan samun karin kaimi a yakin da take yi da muggan laifuffuka da ta’addanci.
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas, ne ya jagoranci mambobin majalisar wajen bikin kaddamar da jiragen a wani mataki na nuna goyon baya.