Najeriya Ta Janye Tallafin Mai Daga Yau Lahadi 1 Ga Watan Janairu.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayinda ya ziyarci inda aka kai hari a wata coci ranar kirsimeti.

Yau lahadi hukumar kayyade farashin mai a Najeriya ta bada sanarwar janye tallafin mai baki daya.

Yau lahadi hukumar kayyade farashin mai a Najeriya ta bada sanarwar janye tallafin mai baki daya.

Ana jin wan nan mataki bashi da farin jinni daga gun ‘yan Najeriya, kasar da tafi ko wacce sayar da mai a ketare a nahiyar.

Irin wan nan yunkuri na cire tallafin mai a shekarun baya ya janyo yajin aiki.

Gwamnati tace janye tallafin mai zai bata damar adana dala milyan dubu takwas a shekara. Wakilan majalisar dokoki sun ce kudade da aka adanan za a yi amfani dasu wajen kara yawan kudade da ake kashewa a ayyukan gina hanyoyi, da kiwon lafiya, da kuma samar da wutan lantarki.

Najeriya tana hakar fiyeda ganga milyan biyu ko wace rana, amma tilas sai ta shigo mai da aka tace daga waje sabo da ta gaza juba jari , da Rashin iya tafiyar da aiki da rashin kayan aiki a matatun man kasar.

Ahalin yanzu kuma tankunan yaki da sojoji ne suke sintiri a wasu sassan arewacin Najeriya bayan da shugaba Jonathan ya ayyana dokar ta baci a wasu sassa da suka fuskanci mummunar hare hare da ake aza laifin kan kungiyar Boko-Haram.

A jiya Asabar shugaba Jonathan ya ayyana dokar ta bacin a yankunan kananan hukumomi 15 cikin jihohin hudu na arewacin Najeriya. Sune, Niger, Flato, Yobe da kuma Borno.