Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman akan al’amuran kafafen sadarwa na zamani Dada Olusegun ne ya bayyana haka a ranar Talata sannan ya bukaci ‘yan Najeriya mazauna Lebann su tuntubi ofishin jakadancin don su ba da bayanan su.
A wani sakon da ya kafa a adireshin shafinsa na X @DOlusegun, mai bai wa shugaban shawara ya ja hankalin duk ‘yan Najeriya da ke Lebanon da “su tuntubi ofisihin jakadancin kasar don ba da bayanansu gabanin a fara kwashe su”.
A ranar Talata, Iran ta harba makamai masu linzami 180 cikin Isra’ila a matsayin martini akan kisan shugabanin Hezbollah.
Kasashen 2 sun yi ta barazana tsakanin su bayan ruwan makamai masu linzamin da Tehran tayi.
Firan ministan Isra’ila Beyamin Netanyahu, ya lashi takobi cewa, Isra’ila zata mai da martini mai zafi akan harin da aka kai mata.
A nasu bangaren kuma, kasar China da Saudi Arabiya sun yi kira da a kwantar da wannan tarzomar da take dada ruruwa a yankin Gabas ta tsakiya sannan, sun yi kira ga bangarorin biyu da su dawo kan teburin tattaunawa.