Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya NCAA, ta ce za ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa a Abuja da Legas.
NCAA ta bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus da ke bazuwa a duniya kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.
Wannan sabon mataki zai fara aiki ne a ranar Litinin 23 ga watan Maris, zai kuma kai har nan da wata guda a cewar wata sanarwa da NCAA ta fitar.
Jaridar Daily Trust wacce ita ma ta tabbatar da labarin, ta bayyana cewa, jiragen da ke jigila a cikin gida za su ci gaba aiki.
A dai ranar Juma’a hukumar ta NCAA ta ayyana dakatar da jigilar jiragen kasa da kasa a filayen jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, Akanu Ibiam da ke Enugu da kuma na Fatakwal da ke jihar Rivers.