Najeriya Ta Cika Shekaru Ashirin Da Kafa Dimokaradiyya

Najeriya ta yi tarihi da cika shekaru ishirin da kafa mulkin damokaradiya, sai dai ra'ayoyin al'ummar kasar sun banbanta dangane da ci gaban da aka samu a kasar cikin shekaru ishirin.

Yayin da ake shirin rantsar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karo na biyu da kuma galibin wasu gwamnonin jihohin kasar, Muryar Amurka ta yi waiwaye maganin mantuwa.

Tsohon Firai ministan Najeriya Abubakar Tafawa Balewa, ya bayyana muradun shugabannin Najeriya, na farko bayan samun ‘yanci, a wani jawabi da ya yi a zauren Majalsiar Dinkin Duniya a shekarar alib da dari tara da casa'in ,inda a lokacin mutane suna magana ne a kan matsayin Najeriya a idon duniya ba matsayin wannan yanki kan wancan, wannan kabila da waccar ko mabiya addinin nan da sauran su.

Abun da ke kara karfafa sahihancin wannan batu shi ne ko bayan yakin basasa daga 1967, shugaban mulkin soja na wancan lokacin Janar Yakubu Gowon ya baiyana yanayin yadda da shugabanni da ma’aikatan gwamnati ko ma talakawa ke tsayawa kan gaskiya da amana don kishin kasa.

Najeriya ta fuskanci tsarin mulki dabam dabam da ya hada da na soja kafin sake komawa mulkin damokaradiya. Tun bayan mulkin soja na Gowon, da ya shafe shekaru 9, sai Janar Babangida ya biyo shi a baya, bayan mulkin Janar Abacha an samu komawa mulkin farar hula a 1999 ta hannun Janar Abdulsalam Abubakar, wanda bayan saukar sa a mulki ya rungumi aikin hada kan manyan ‘yan takarar siyasa don amincewa da komawa mulkin damokaradiya da rungumar harkokin siyasa.

Janar Obasanjo ya yi rantsuwar karbar mulki bayan fitowar sa daga gidan yari da kaddara ta sa ya yi mulki har ya sauka a 2007 marigayi Alhaji Umar ‘yar adua ya hau mulki.

Bana shekaru 20 da dawowa wannan jamhuriya inda shugaba Buhari da ya yi mulkin soja ya samu wa’adi na biyu a farar hula.

Domin karin bayani saurari rahoto na musamman.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Cika Shekaru Ashirin Da Kafa Dimokradiyya