Darakta-Janar na hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta kasar (NITDA) Kashifu Inuwa Abdullahi, ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na bude babban taron samar da sabbin dabaru da binciken manhajojin kasuwanci a Najeriya na shekarar 2021.
Kungiyar daliban ilimin kimiyar nau’ra mai kwakwalwa (NACOS) ce ta shirya taron, tare da haɗin gwiwar hukumomi da kamfanonin hada-hadar kudi na fasahar zamani, tare da zummar zakulo matasa masu hazaka da dabarun amfani da na’ura mai kwakwalwawajen taimakawa kasar a fagen samar da sabbin hanyoyi masu sauki.
Jami’ar Nile da ke Abuja ce ta karbi bakuncin taron da aka yi wa take da ’‘yadda za’a hada kai da matasa wajen amfani da fasahar zamani don kirkiro abubuwa na mussaman da kuma lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ci gaba a kwarewar aiki’’
Shugaban hukumar NITDA ya karfafawa matasa da su yi amfani da wannan damar wajen tallata hajarsu ta abubuwan da suka kirkiro zuwa kayayyaki da aiyukan da za'a iya kasuwanci da su.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kirkiro wasu shirye-shirye da dabaru da tsare-tsaren da za su taimakawa kasar da kuma ba ta damar samarwa matasa yanayin bunkasa ilimin fasaharsu da kirkirar manhajoji na cikin gida da zu taimakawa kasar.
Wadannan shirye-shiryen a cewar sa, za su samar da hanyar samun kudi ga matasa a kasar masu hazaka da basirar kirkira bayyanasu ga duniya.
Kazalika yabayyana cewa hukumarsa na aiki tukuru tare da babban bankin Najeriya da wasu hukumomin gwamnati don hada kudi ga matasa a kasar su inganta ayyukansu na kirkira, ya na mai cewa suna aiki tare da wasu jami’o'i a kasar wajen zakulo matasan.
Shigowar Annobar COVID-19 Najeriya a cewar Kashifu, ya samar da wata dama ga matasa a kasar na amfani da fasahar da su ka kirkiro wajen fara sabbin sana’oi da tallata hajarsu.
Ya ce a aikin shirin hukumar NITDAna shekarar 2021 zuwa 2024 ya fitar da tsare-tsare da matasa za su shiga don inganta ayukansu.
Your browser doesn’t support HTML5