Gwamnatin tarayya ta bukaci hukumar ‘yan sandan kasa da kasa ta INTERPOL ta sanya idanu akan wasu ‘yan Najeriya uku akan zargin yin takardun bogi.
Majiyoyi sun bayyana cewar ana neman wadanda ake zargin-wani jami’in babban bankin Najeriya, Odoh Ocheme da wasu mutane biyu ruwa a jallo ne akan zargin kwaikwayar sa hannun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari domin satar fiye da dala milyan 6 da dubu 200 daga babban bankin.
Ana zargin Ocheme da kitsa almundahanar tare da yin takardun bogi da sunan Shugaba Buhari domin wawure fiye da dalar amurka milyan 6 da dubu 200 daga asusun babban bankin Najeriya, tare da Adamu Abubakar da Imam Abubakar.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mukaddashin Kwamishinan ‘Yan Sanda kuma Shugaban Sashen Kula da Ayyuka da bincike na musamman a rundunar ‘yan sandan Najeriya, Oloho Okpoziakpo.