Najeriya Ta Bi Sahun Kasashen Da Suka Datakar Da Amfani Da Jirgin Boeing

Wani jirgin saman Najeriya na tsohon kamfanin kasar, Nigeria Airways

Duk da cewa ba ta mallaki wannan nau’in jirgi na Boeing 737 Max 8 da 9 a kasar ba, Najeriya ita ma ta bi sahun sauran kasashen da suka dauki matakan dakatar da amfani da jirgin bayan hatsarin kasar Habasha.

Ministan Ma’aikatar Sufurin jiragen sama a Najeriyar, Hadi Sirika, ya ce duk da cewa sararin samaniya mallakin duniya ne amma ya zama dole dauki wannan mataki.

"Da yake ka san cewa ita harkar sufurin jiragen sama, ta duniya ce bai daya, ba ta kasar Najeriya ba ce kawai, amma baayn an smau wannan hatsari a Habasha, abin da muka yi kokarin yi shi ne, duk jirgi samfurin wannan Boeing 737 Max 8 da 9, kar su ta shi kar kuma su sauka a Najeriya."

Ya kara da cewa, "kuma cikin hukuncin Allah, babu wani da yake da irin wannan jirgi a Najeriya." Sirika ya fada a wani taron manema labarai.

A jiya Laraba, shugaban Amurka Donald Trump, ya dakatar da amfani da nau’in jirgin saman samfurin Boeing da ake kerawa kasar.

"Amurka na da kyakkyawan tarihi idan ana magana akan matakan kiyayen hadurra a fannin zirga zirgar jiragen sama, muna kuma so tarihin ya dore, saboda haka, ba na so na yi sako-sako da wannan lamari.” Trump ya ce.

Wannan mataki da Amurkan ta dauka, shi ne mafi girma cikin jerin kasashen da ke daukan matakan dakatar da amfani da jirgin.

A baya bayan nan, China, Habasha, Turkiyya, Brazil, Korea ta Kudu da daukacin kasashen da ke tarayyar turai, sun dakatar amfani da jirgin na wani lokaci.

Kididdigai dai ta nuna cewa, kafin aukuwar wannan hadari na Ethiopia, akwai akalla nau’in wannan jirgi 400 da suke aiki a duk fadin duniya.