Najeriya: Rikicin Boko Haram Ya Kassara Ilimin Yara Fiye da Miliyan Daya

Irin yaran da rikicin Boko Haram ya hanasu samun ilimi

A Najeriya fiye da yara miliyan daya ne ciki da kewayen kasar tashe tashen hankula suka kassara neman ilminsu, kari kan yara milyan 11 wadanda basa makaranta a yankin.

Kamar yadda asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana jiya Litinin, fiyeda makarantu dubu biyu a fadin Najeriya da Kamaru da Cadi, da Nijar ne aka rufe tun sa'adda aka fara rikicin Boko Haram, wanda ya dagula la'amura a yankin, ya kuma raba miliyoyin jama'a da muhallansu.

Rikicin, inji darektan asusun mai kula da shiyyoyin Afirka ta yamma da Afirka ta Tsakiya- Manuel Fontaine, yayi mummunar illa ga harkokin Ilmi. Fontaine yace rikicin ya hana yara masu yawa zuwa makaranta fiyeda shekara guda,lamari da ya jefa su cikin hadari barin makaranta baki daya.

NIGERIA BORNO BOKO HARAM IN BAMA