Wasu jihohin Jamhuriyar Nijar da na Najeriya, sun tattaunaw kan batutuwan da suka shafi tsaro, bayan da aka samu bullar wasu mutane dauke da makamai akan iyakokin ksashen biyu.
Magatakardan ofishin gwamnan jahar Dosso, ya yi kira ga jahohin da su tashi tsaye domin kafa rundinar tsaro a yankunan.
Bayan samun labarin wadansu mutane da a ke zaton yan ta'adda ne, da suke aikata wadansu dabi'u da ba daidai ba a iyakar Nijar da Najeria,a wani gari da a ke kira da Jima - Jimi a cikin karamar hukumar mulkin Tangaza ta jahar Sokoto.
An kwashe kwanaki biyu ne ana gudanar da wannan taron domin yin dubi akan hanyar da za'a samar da kariya a tsakanin Dosso da Tahoua da ke kasancewa mafaka ga masu aikata miyagun laifuka
Gwamna Jihar Sokoto Amina Waziri Tambuwal, ya ce wannan babban lamarin ya haifar da fargaba wa 'al'umomin da ke kewaye da Jima-jimi ta karamar hukumar Tangaza da ke cikin jahar Sokoto.
Your browser doesn’t support HTML5