Najeriya Na Shirin Yi Wa Duk Yan Kasa Rigakafin COVID

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta samar da kayan aiki don tabbatar da duk wani dan Najeriya ya sami rigakafin COVID.

Gwamnatin tarayya ta jaddada aniyar samarda duk abinda ake bukata don ‘yan Najeriya su sami allurar rigakafin cutar Corona.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha ne ya bayar da wannan tabbacin a taron masu ruwa da tsaki na jihohi shida a Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Town Hall

Shugaban komitin yaki da cutar Corona kuma sakataren gwamnatin tarayya, Mr. Boss Mustafa ya bayyana hakan yayin taron fadakar da masu ruwa da tsaki a jihohi shida dake shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya, da aka gudanar a garin Lafiya, fadar jahar Nasarawa.

Town Hall 2

Gwamnan jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule wanda ya zayyana irin matakan da gwamnatinsa ta dauka wajen yaki da cutar Corona ya kuma ce gwamnatin tasa ta kaddamar da cibiyar gwaji kan cututtuka masu yaduwa inda ake gwajin rigakafi da magunguna.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Ce Za Ta Samar Da Kayan Aiki Don Tabbatar Da Duk Yan Najeriya Sun Samu Rigakafin COVID