Wata sanarwa ta fito daga fadar shugaban Najeriya, zuwa ga manema labarai, da ke cewa Shugaba Mohammadu Buhari ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Ministan harkokin cikin gida, Ra'uf Aregbesola wanda zai yi nazarin sabbin ka'idojin da Amurka ta gindaya, da suka shafi batun tsaro da ake bukatar gwamnatocin kasashen waje su rika bi.
Dalilin da Amurka ta bayar shi ne Najeriya ba ta cika ka'idojin tsaro, da rashin bayar da hadin kai wurin magance tafiye-tafiye tsakanin kasashe ba bisa ka'ida ba.
Tsohon jakadan Najeriya a Sudan Suleiman Dahiru ya ce Amurka ta yi dai-dai wajen daukar matakin da ta yi, domin akwai wasu bata gari wadanda ba sa daukar kasar da mutunci.
Amma ya bada shawarar a yi kokari a tantance dukkanin masu neman barin Najeriya da neman shiga Amurka.
Koda yake yunkurin kafa kwamitin da Najeriya ta yi na nuna cewa a shirye ta ke, ta ci gaba da karfafa kyakkyawar alaka tsakanin ta da Amurka, da sauran kawayenta na kasashen waje musamman akan harkokin tsaro a duniya, saboda kwamitin zai yi aiki ne tare da gwamnatin Amurka da 'yan sandan kasa da kasa wato Interpol da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwararre a harkar zamantakewar dan Adam kuma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum Mohammed Ishaq Usman, ya ce wannan umurni da kasar Amurka ta bada na takaita 'yan Najeriya takardar Visa ita ce za ta yi hasara.
Ya kuma yi kira ga 'yan majalisar dokokin Amurka da su sa baki a al'amarin saboda a samu dai-daito don kada a wulakanta 'yan Najeriya.
Shi ma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Jam'iyar PDP a shekara 2019 Atiku Abubakar ya nuna takaicin sa kan lamarin.
A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5