Nahiyar Afirka na da kasashen da ke bunkasa sosai a fannin fasahar zamani a fadin duniya, kuma sannu a hankali Najeriya na zama babbar cibiyar fasaha a nahiyar.
Najeriya dake yammacin Afirka, ta yi kaurin suna wajen abubuwa marasa kyau, da suka hada da rashawa da kuma ta'addanci da ke ci gaba da kasancewa manyan matsaloli. Kuma ta yiwu abin da ya sa gwamnatin Trump daukar mataki akan baki daga kasar kenan a kwanan nan.
Duk da haka, akwai abubuwa masu kyau game da kasar, ban da batun Boko Haram ko kuma wani yariman karya mai dukiya da yawa dake yaudarar mutane.
Najeriya ta zama wata babbar cibiyar 'yan kasuwa, kuma wani dandalin kafa kananan kamfanoni, ta zama wata hanyar kutsawa cibiyar Silicon Valley ta Amurka kuma.
A matsayin kasuwar dake gaba-gaba, kawai matsaloli da yawa a tattare da siyasa da tattalin arzikin kasar.
Duk da wadannan matsalolin, 'yan kasuwa a fannin fasaha da yawa daga Amurka da China da kuma wasu kasashen Afrika na kwadayin zuwa Najeriyar.