Najeriya Na Duba Yiwuwar Sake Bude Kan Iyakarta, Abin Da Ya Janyo Muhawara

Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Yayin da gwamnatin Najeriya ke nazarin yiwuwar sake bude kan iyakarta don hada hadar cinakayya da sauransu, 'yan kasar sun shiga muhawara kan alfanu da kuma rashin alfanun yin hakan.

Bayyana shirin gwamnatin Najeriya na bude kan iyakar kasa don dawo da hada-hadar kasuwanci na samun mabambantan ra'ayoyi, kama daga masu cewa hakan daidai ne zuwa masu cewa a'a, ci gaba da rufe kan iyakar ya fi alfanu.

Gwamnatin Buhari, fiye da shekara daya da ta wuce, ta rufe kan iyakar da kafa hujjar cewa don hana shigo da makamai ne ga 'yan ta'adda da kuma dakile simoga.

Ministar kudi, Zainab Shamshuna ta ce kwamitin da ta ke jagoranta na batun bude kan iyakar zai mika rahotonsa ga Shugaban kasa don daukar matakin da ya dace.

Duk da Shamsuna ba ta fadi takamammiyar ranar bude iyakar ba, ta ce tuni ta sanya hannu kan rahoton, inda sauran 'yan kwamitin za su bi sahu. Masana tattalin arziki irin Yushau Aliyu da ke Abuja, na da ra'ayin cewa rufe kan iyakar zai kara kuncin tattalin arziki ne.

Ga babban manomi, Sanata Abdullahi Adamu, bude kan iyakar zai kawo koma baya ne ga nasarar da a ka samu ta noma abinci a cikin gida.

Ko da lokacin da a ka rufe kan iyakar tun can farko, an bar hanyoyin shigowa da kaya ta teku da shugaban hukumar kwastam, Kanar Hamid Ali ya ce don nan ne ke da na'urorin gwajin ingancin kaya.

Batun rufe iyaka ya sanya masu sharhi daga arewa, in ka debe manoma, nuna hamayya da lamarin da cewa ya kawo takurawa da maida yankin koma baya.

Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Na Nazarin Yiwuwar Sake Bude Kan Iyakarta