Najeriya Na Dab Da Soma Sarrafa Na Ta Rigakafin Korona

  • Murtala Sanyinna

NAFDAC

Abin da kawai gwamnatin Najeriya ke jira domin ta soma sarrafa na ta alluran rigakafin cutar COVID-19, shi ne amincewar hukumar lafiya ta duniya – WHO.

Yayin da take jawabi a wani taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki da majalisar wakilai ta shirya, shugaban hukumar kula da sahihancin abinci da magunguna ta Najeriya – NAFDAC, Moji Adeyeye, ta ce hukumar lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya tana nan tana tantace hukumar ta NAFDAC, domin ba ta iznin sarrafa rigakafin na corona a cikin Najeriya.

Ta ce an soma aikin tantancewar ne a ranar Litinin, ana kuma sa ran kammalawa zuwa ranar Juma’a ta wannan makon.

A lokacin taron, Ministan kwadago Chris Ngige ya yi kira ga ‘yan majalisar dokokin da su hanzarta aikin zartar da kudurin dokar aikin kula da kare lafiyar a’umma.

Ita kuwa daraktar sashen kariya daga haduran aiki da lafiya a ma’aikatar, Lauretta Adogu, ta yi alkawarin tabbatar da samar da sahihan ka’idodin kariyar ma’aikata a wuraren aiki.

Ta ce idan aka zartar da kudurin dokar, zai samar da samar da ingantaccen kariyar lafiya a wuraren aiki da saura lamurra.

Haka kuma hukumar za ta ba da damar kafa majalisar kula da kariyar lafiyar ma’aikata, ta kuma warware matsaloli da dama, domin kuwa za ta yi aiki ne a dukan wuraren aiki.