Najeriya Na Bayan Kasashe Arba'in Kan Cigaba Da Rayuwar Jama'a

Shugabannin kasashen cikin kungiyar Tarayyar Afirka a wurin taron

A taron Kungiyar Afirka a Dakar babban birnin Senegal kungiyar da hadin kan Gidauniyar Mo Ibrahim ta gabatar da rahotonta kan cigaba ko komabaya da kasashen suka samu a shekara da ta gabata
Cikin rahoton da Kungiyar Afirka ta fitar a wurin taronta na shekara da tayi a kasar Senegal alkalluma sun nuna Najeriya ta samu komabaya a cigaban kasa da rayuwar jama'a.

Rahoton hadin gwuiwa na Kungiyar Afirka da Gidauniyar Mo Ibrahim ya nuna cewa a cikin kasashe 52 dake cikin kungiyar, Najeriya ce tazo ta 41 wurin samun cigaba da kyautata rayuwar jama'a yayin da makwafciyarta Niger ta zo ta 28.

Wakilin Muryar Amurka Nasiru Ibrahim El-Hikaya ya zanta da masani domin ya san musabbabin wannan komabayan da kasar ta samu. Ya ce kowace shekara Gidauniyar Mo Ibrahim tana fitar da rahoto game da abun da ya shafi gudanar da mulki da tattalin arziki da tsaro da jin dadain jama'a da zamantakewa na kowace kasar Afirka. Ya ce an kawo rahoton gaban manyan shugaban Afirka inda Najeriya itace ta zama ta 41 cikin kasashe 52.

Kasashe da yawa sun samu cigaba amma banda Najeriya. A zahirin gaskiya ma komawa baya tayi musamman kan zaman lafiya da mulki na gari. Sabili da haka akwai kasashe 40 a gaban Najeriya wajen cigaba. Ko kasashen da Najeriya take gabansu banbancinta da su bai taka kara ya karya ba. Amma akwai tazara tsakaninta da kasashen dake gabanta. Yawancin kasashen dake gaban Najeriya kasashe ne da suke cikin fitinu, wato su ma suna fama da rashin zaman lafiya amma duk da haka sun samu cigaba kamar irin su Somalia da Kwango Kinshasha. Wasu kasashen dake makwaftaka da Najeriya sun sha gaba, kamar su Niger da Jahuriyar Benin da Ghana da Mauritania da Botswana ma wasu.

Rahoton ya kara da cewa a Najeriya yara fiye da miliyan goma sha daya da suka isa zuwa makaranta basa zuwa domin babu makarantun. Wanna rahoton komawa baya ne. Yakamata shugabanni su damu su san yadda zasu yi su kawo cigaba. Kada su bar rikici da fitina su zama dalilin rashin cigaba. Ya makata rahoton ya tada kasar daga barci.

Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Na Bayan Kasashe Arba'in Kan Cigaba Da Rayuwar Jama'a - 2:42