Ana ‘yan sa’o’i kungiyar kwadago ta fara zanga-zanga a fadin Najeriya saboda abin da kungiyar kwadagon ta kira rashin aiwatar da yarjajjeniyar biyan Naira dubu 30 a matsayin albashi mafi kankanta a Najeriya, kungiyar kwadagon ta NLC da gwamnatin Najeriya sun cimma amincewa da Naira dubu 30 (N30,000) a matsayin albashi mafi kankanta a Najeriya kamar yadda kungiyar ta NLC ta bukaci a yi.
Cimma wannan jituwar ya biyo bayan tattaunawa mai sarkakkiya da kuma daukar lokaci ne da aka yi tsakanin bangarorin biyu, abin da ya kai ga nasarar kawar da barazanar fara yajin aikin daga yau Talata.
Tuni jami’in yada labaran kungiyar ta NLC komred ya tabbatar ma wakilinmu ta wayar tarho cewa, ba za a tsaya nan ba, za a tura ma Shugaba Nuhammadu Buhari yarjajjeniyar da aka cimma din don shi kuma ya tura ma Majalisar Dokokin Tarayyar najeriya, wadda ita kuma za ta rattaba hannu don ta tabbata a hukumance.
Ga dai wakilinmu a Abuja, Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5