Najeriya: Mutum 150 Suka Mutu Sakamakon Cutar Coronavirus

Rahoton baya-baya na cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ya nuna cewa an samu sabbin mutum 242 da suka kamu da cutar coronavirus.

Hakan ya sa gaba dayan adadin wadanda cutar ta harba a kasar yanzu ya kai dubu hudu da dari shida da arba'in da daya. 4,641

Jihohin da aka samu karuwar masu cutar sun hada da Legas inda mutuum 88 suka harbu, 64 a Kano, 49 a Katsina, 13 a Kaduna, tara a Ogun, shida a Gombe, hudu a Adamawa, sai kuma birnin tarayya Abuja inda aka samu mutum uku.

An samu karin mutum daya-daya a jihohin Ondo, Oyo, Rivers, Zamfara, Borno da kuma Bauchi da cutar ta kama.

Ya zuwa daren ranar Litinin 11 ga watan Mayu, mutum 902 ne suka warke daga cutar a kasar, yayin da mutum 150 suka rasa rayukansu sakamakon cutar.