Najeriya: Majalisa Za Ta Rage wa Masana'antu Radadin Coronavirus

Jami'an tsaron da aka girke a kofar shiga majalisar dokokin Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta dauki wani mataki da zai rage wa masana'antu radadin karyewar tattalin arziki a sakamakon dakatar da ayyuka domin gudun yaduwar cutar Coronavirus a ma'aikatunsu.

A zaman majalisar abin mamaki shi ne, cikin sa'a daya kuma tashi daya, majalisar ta tattauna batun matsalar da bangaren masana'antu da ma'aikatansu ka iya fuskanta a wannan lokaci da Najeriya ta bi sahun kasashen duniya wajen kokarin magance yaduwar cutar Coronavirus.

Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da kudurin da kansa kuma wannan shi ne karo na farko a tarihin Majalisar Wakilan da za a samu irin wannan yunkuri.

Gbajabiamila ya nuna cewa muhimmin abin da dokar za ta yi shi ne dauke haraji akan magunguna da marasa lafiya ke bukata, da kayayakin aikin asibiti da kayan da jami'an kiwon lafiya za su yi amfani da su a matakan duba lafiyar al'umma a lokuta daban-daban.

Bayan kammala wannan aiki ne majalisar ta bi sahun yan'uwanta da ke majalisar dattawa ta dage zamanta har sai zuwa ranar 7 ga watan Afrilu, wani abu da Honorable Abubakar Hassan Fulata ya ce hutun jaki ne da kaya.

A cewar Fulata, za su bazama ne zuwa mazabunsu su yi aikin wayar da kan al'ummansu akan wannan mummunar cuta da yanzu ke razana manyan kasashe da kuma kanana.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasa da hukumar kula da cututtuka masu yaduwa na daukan matakan gwaji akai-akai domin sanin adadin wadanda cutar ke yi wa barazana a kafofin shige da fice a birnin tarayya.

Saurari cikakken rahoton a sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Majalisa Za Ta Rage wa Masana'antu Radadin Coronavirus