Wata kotu a Najeriya za ta fara sauraren shari’ar kamfanin Binance, mai hada-hadar kudin intanet na crypto kan kin biyan haraji a ranar 11 ga watan Oktoba mai zuwa, kamar yadda alkalin da ke sauraran karar ya bayyana a ranar Juma’a.
Kamfanin na Binance na fuskantar tuhume-tuhume guda hudu na kin biyan haraji, da suka hada da gaza yin rajista da hukumar tattara kudaden shiga ta Najeriya don biyan haraji.
An kuma janye irin wadannan tuhume-tuhume a kan biyu daga cikin shugannin kamfanin a ranar 14 ga watan Yuni, ko da yake har yanzu suna fuskantar tuhume-tuhume daban-daban na halatta kudade haram.
Sai dai dukkansu sun musanta wadannan zarge-zarge.
Wakilin Binance Ayodele Omotilewa ya gurfana gaban kotu a ranar Juma’a kuma ya ki amsa laifuka hudun da ake tuhumarsa da su a zaman da aka yi a gaba alkali Emeka Nwite.
Sai dai kamfanin Binance bai ce komai ba nan take, amma ya fada a baya cewa ya kamata a yi watsi da tuhume-tuhumen.
Najeriya dai ta zargi Binance bayan da shafukan intanet na hada-hadar kudin intanet na crypto suka zama hanyoyin da ake amfani da su wajen kasuwanci da Naira ta Najeriya, a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar karancin dala da faduwar darajar kudinta.
Reuters