Manazarta kan harkar tsaro a Najeriya sun ce suna goyon bayan a duba yiwuwar halatta wani shiri na samar da doka wacce za ta bayar da ikon kafa wata hukuma ta musamman da za ta yi mu'amala da yan ta'adda.
Hukumar za ta kuma tsugunar da tubabbun ‘yan ta’addan ta hanyar sauya musu hankali da basu horo kan koyon ayyukan hannu saboda dogaro da kai.
Manazartan na tunanin yin haka zai kawo karshen yakin ta'addanci da a halin yanzu ya yi wa shiyyar Arewa maso Gabashin kasar katutu har na tsawon shekara 10.
Wannan ce-ce ku-ce dai ya biyo bayan wani kudurin doka da tsohon Gwamnan Jihar Yobe, wanda a yanzu ya ke matsayin sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas ya kawo gaban Majalisar Dattawa.
Kudurin dai na cewa a kafa wata hukuma da za ta kula da tubabbun yan ta'adda da kuma wadanda suke so su ajiye makamansu.
Tuni har an yi wa kudurin dokar karatu na farko.
Wani lauya mai suna Ibrahim Arab ya shaida wa wakiliyarmu Medina Dauda cewa a duk duniya ana yin irin wanan yunkurin tare da yin sulhu da yafiya saboda a kawo karshen yaki.
Ya kawo misalin yadda Amurka ta yi sulhu da ‘yan ta'addan Taliban a kasar Afganistan da kuma irin yafiyar da marigayi Nelson Mandela ya yi wa wadanda suka tozarta shi, wanda a dalilin haka ne kasar Afrika ta Kudu ta samu cigaba da habbakar tattalin arziki.
To sai dai kwararre a fannin diflomasiyyar kasa da kasa kuma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum Mohammed Ishaq Usman, ya ce “babu kasar da ta san abinda ta ke yi da za ta yarda ta yi sulhu da ‘yan ta'adda, saboda ai maciya amana ne su”.
Wannan lamarin na faruwa ne a dai dai lokacin da wasu 'yan Boko Haram da dama ke ta mika wuya ga dakarun tsaro a Najeriya.
A jiya ma wasu mayakan ‘yan asalin kasar Chadi su biyu sun yi saranda.
Saurari wannan rahoton a sauti daga bakin wakiliyarmu Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5