Babban lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya kuma Ministan Shari’ar Kasar, Lateef Fagbemi, yayi jan kunne game da sabawa hukuncin kotun koli a kan ‘yancin gashin kan kananan hukumomi, inda ya sha alwashin hukunta jami’an da suka karya dokar.
Fagbemi ya yi jan kunnen ne a jiya Alhamis a Abuja a jawabinsa ga taron ‘yan jarida masu daukar rahotannin kotuna da bangaren shari’a.
A cewar antoni janar din, shugabancin a matakin kananan hukumomi ya sha wahala a baya sai dai ya yi imanin cewa idan aka tursasa amfanin da hukuncin ‘yancin kananan hukumomin, “rayuwa za ta inganta a kananan hukumomin.”
A watan Yulin da ya gabata, kotun kolin Najeriya ta zartar da muhimmin hukuncin da ya tabbatar da ‘yancin kananan hukumomi na sarrafa kudadensu. Hukuncin ya dakatar da gwamnonin daga yin tasrifi da kudaden kananan hukumomin.
Haka kuma ya umarci antoni janar din tarayya ya rika biyan kudaden kananan hukumomn kai tsaye cikin asusun ajiyarsu a wani yunkuri na karfafa ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomin a fadin Najeriya