A yau Alhamis shugaba Buhari ya fara ziyarar aiki ta wuni daya bayan haka gobe Jumma’a idan Allah ya kai mu zai halarci tattaunawar kungiyar nan ta kasashe masu matsakaicin karfi guda takwas, kasashen da suka hada da Malaysia, da Pakistan da Bangladesh, da Masar da Indonesia, da Iran, da Turkiyya da kuma Najeriya.
A ganawar da shugaba Buhari yayi yau da takwaransa na kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan, sun amince akan yaki da ta’addanci da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen guda biyu.
Kakakin fadar shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya shaidawa wakilin sashen Hausa Umar Faruk Musa cewa, muhimman abubuwa guda uku ne ke a agendar shugaba Buhari a wannan zayarar.
Ya ce abu na farko shine neman hadin kai da goyon bayan juna akan yaki da ta’addanci saboda ayyukan ta’addanci sun shafi kasashen biyu. Turkiyya na fama da mayakan ISIS, Najeriya kuma na fama da ‘yan kungiyar boko haram. Bayan haka kuma akwai masu tada kayar baya na cikin gida da kasashen biyu ke fama da su, da suka hada da ‘yan IPOB a Najeriya da kuma wadanda suka so yin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya cikin shekarar da ta gabata.
Bayan haka, a cewar Malam Garba Shehu, batun tattalin arziki na cikin abubuwan da za su tattauna a akai, saboda akwai bukatar a nemo masu zuba jari a Najeriya, ta hanyar bude masana’antu da zasu kawo cigaba ta bangarorin noma, da ilimi, da sufuri, da sadarwa da kuma bangaren man fetur.
Garba Shehu ya kuma ce, kasar Turkiyya ta amince ta tura masu zuba jari a fannin man fetur. Kasar kuma ta kulla yarjejeniya akan horror da sojojin Najeriya da kuma habbaka masana’antar kera makaman soja dake jihar Kaduna da ake kira DICON a takaice. Bayan haka akwai yarjejeniyar da ta shafi ilimi, ta fannin musayar dalibai, da malaman jami’o’i da sauransu.
Garba Shehu yace kasashen biyu na fatan kara fadada dangantakarsu yayinda yarjeniyoyin suka fara aiki.
Za ku ji karin bayani a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5