Najeriya da Nijar Suna Shirin Bunkasa Kasuwanci Tsakaninsu

Muhammadu Buhari na Najeriya da shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar;

Jami'an kasashen Nijaeriya da Nijar suna ganawa kan shirin bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu

Ganawar ta yau ta biyo bayan taron da suka yi ne kan iyakokin kasashen dake tsakanin jihar Sokoto a Najeriya da Tawa a Nijar.

A shirin na bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen za'a gina wuraren ajiye kaya a bakin iyakokinsu. Za'a gina daya a iyaka dake tsakanin Kamba ta jihar Kebbi da jihar Dosso dake Nijar.

Hakazalika za'a gina daya a Matamaye dake Nijar da kuma Daura dake Najeriya kana a gina daya a Maradi da Katsina.

Za'a kuma gina daya a Illela ta jihar Sokoto ba birnin Kwanni a jihar Tawa cikin Nijar.

Da zara an kammala gine ginen wuraren kasashen zasu iya ajiye kaya abakin iyakokinsu.

Duk wani mai bukatar sayen kayan Najeriya baya bukatar yin tattaki zuwa Legas ko Kano ko Onitsha da wasu wuraren. Sai dai ya sayi kayansa a bakin iyakokin kana ya biya harajin da yakamata.

Hakazalika duk masu bukatar sayen kayan Nijar basu bukatar zuwa garuruwan Maradi ko Agades ko Niamey. Saidai su sayi kayansu a bakin iyaka bangaren Nijar su ma su biya duk harajin da yakamata..

Akan wannan shirin Alhaji Sani Mai Kaso yayi karin bayani. Yace 'yan kasuwa sun yi murna da shirin. An kawo kasuwa kusa kusa ba sai an yi tafiya da nisa ba. Banda haka su gwamnonin zasu fi samun kudin shiga fiye da yanzu.

Shi ma Yusuf Haruna Zinder shugaban 'yan kasuwa na Illela jihar Sokoto ya nuna gamsuwarsa da alfanun da za'a samu. Yanzu gwamnatin Najeriya ta gaskiya ce da adalci.

Shirin ya hada da gina layin dogo daga Sokoto zuwa Illela saboda jigilar kaya. Kowa zai anfana kuma matasa zasu samu aikin yi matuka.

Ga rahoton Haruna Bako.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya da Nijar Suna Shirin Bunkasa Kasuwanci Tsakaninsu