Najeriya Da Morocco Sun Tsaida Yarjejeniyoyin Harkokin Kasuwanci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Sarkin Morocco Mohammed VI

Yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Sarki na Morocco Muhammad na 6 suka rattaba hannu akan wata yarjejeniya kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi ayyukan noma da tattalin arziki. Daga Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya hada mana rahoto dangane da kunshin yarjejeniyar

Sanya hannu akan yarjeniyoyin ya biyo bayan ziyarar yini biyu da shugaba Buhari ya kai kasar ta Morocco ne wadda ya kammala a yau din nan litinin.

Batutuwan da shugabannin biyu suka amince akansu sune, batun shimfida bututun iskar gas da zai baiwa najeriya damar samar da albarkatun iskar gas ga kasashen Afrika ta yamma wadda zai ratsa ta Morocco ya wuce kana zuwa nahiyar turai.

Aikin shimfida bututun wadda aka tsara zai wakana a cikin shekaru 25 masu zuwa, bayan kammala shi zai bada damar cimma bukatun albakatun iskar gas ga al’umomin kasashen da zai keta ta cikin su da kuma wadanda ke zirga-zirgar sufuri a nahiyar.

Kunshin yarjejeniyar ya nuna aikin shimfida iskar gas din nada tsawon murabba’in kilomita dubu 5 660 kuma zai rage asarar iskar gas da najeriya keyi, baya ga karfafa tsarin fadada hanyoyin samar da makamashi ga ‘yan najeriya, yayain da a hannu guda kuma, zai saukaka radadin talauci tare da samar da guraben ayyuka ga ‘yan kasa.

Bugu da kari, aikin shimfida bututn iskar gas din daga najeriya ya keta wasu kasashen Afrika ta yamma ya bi ta Morocco zuwa Turai zai dakushe barazanar hamada a yankin Sahel na Afrika.

Baya ga batun shimfida batututun gas, najeriya da Morocco sun amince akan wata yarjejeniya da zata dafawa najeriyar kafawa tare da bunkasa masana’antar sarrafa sinadarin alkaline wadda zai maida hankali wajen harhada takin zamani da dangoginsa.

Sai kuma, wata yarjejeniyar aiki tare domin inganta ayyukan cibiyoyin lamuran bada horo kan dabarun sarrafa kayan noma a najeriya.

A wata sanarwar da kakakin shugaba Buhari ya fitar tace shugaban na najeriya ya nanata aniyar gwamnatin sa wajen aiwatar da yarjeniyoyin domin cimma burin da aka sanaya a gabata.

Batun hanyoyin ingantawa da cinikayyar amfanin gona na daga cikin kunshin yarjejeniyar da shugaba Buhari ya cimma da takwaran sa Amurka Donald Trump a yayin ziyarar da shugaban na najeriya kai Amurka cikin watan jiya.

Yarjeniyoyin da najeriya ke kullawa da kasashe musamman game da batutuwan da suka shafi ayyukan noma da cinikayyar amfanin gona, na zuwa a dai-dai lokacin da manoman kasar ke kokawa game da karancin tallafin gwamnati ta fuskar samar da kayayyakin noma, bayan da tuni suka amsa kiranta na komawa gona domin wadata kasa da abinci.

Saurari Rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Matsaya da Najeriya ta Cimma Da Morocco-2:30"